ABNA24 : Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto Aruwan yana fadar haka a jiya jumma’a ya kuma kara da cewa, da farko ‘yan bindigan sun kashe wani mutum wanda ake kira Irmiya Godwin a lokacinda shi da dan’uwanda suke dawowa daga gona a kauyen Gora Gan a karamar hukumar Zangon Kataf, amma dan’uwansa ya tsira daga harin, sannan sun kashe mutane 10 a garin Kizashi na karamar hukumar Kaura banda haka sun kona gidaje 56 da babura 16. Kwamishin ya kammala da cewa wadanda aka kashe sune
Esther
Bulus, Maria Bulus (dan shekara guda diyar Esther), Lami Bulus, Aliyu Bulus,
Monday Joseph, Geje Abuba, Wakili Filibus, Yakubu Ali., Dije aziri, Joseph
Ibrahim .
Sannan wadanda suka ji rauni kuma sun hada da : Cecilia Aku, Yakubu Idi, Godiya Saleh da kuma Moses Adamu.
342/